Aminu Mahmoud and Brothers Nig. Ltd

Aminu Mahmoud and Brothers Nig. Ltd AMINU MAHMOUD AND BROTHERS NIGERIA LIMITED IS A CONSTRUCTION COMPANY ON ROAD, BIULDING AND BORE HOLES

18/12/2020

An samu wata yarinya 'ƴar shekara 14 da cutar HIV bayan mutane 9 sun yi ma ta fyaɗe a wani kauyen karamar Hukumar Mai'adua ta jihar Katsina.

Daga : Janaidu Amadu Doro.

Rundunar 'Ƴan sandan jihar Katsina ta baje kolin masu laifuka daban-daban da s**a haɗa da masu sata da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da 6arayin ababen hawa da masu yi wa ƙananan yara fyaɗe da sauransu.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya yi holen ma su laifin, a jiya Laraba a farfajiyar Shelkwatar da ke Katsina.

A yayin holen, Gambo Isah ya ce, a cikin masu laifin har da wasu mutane tara da ake zargin su da yi wa yarinya mai shekaru 14 fyaɗe, mai suna Auwa Mato a karamar hukumar Mai'adua da ke jahar Katsina.

SP Gambo ya ce, mahaifin yarinyar, Mu'azu Yakubu ne a ranar 6 ga watan 11 na shekarar 2020 ya je ofishin 'Ƴan sanda na Mai'adua ya kai ƙarar waɗanda ake zargin kuma dukkan su sun fito ne daga kauyen Kwadage da ke karamar hukumar, haka kuma dukkansu sun amsa laifinsu cewa sun yi lalata da yarinyar.

Sai dai a yayin da Rundunar 'Ƴan sandan ta tura mutanen 9 da kuma yarinyar zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu an samu mutum ɗaya a cikinsu mai suna Shafi'u Mamman wanda ya ke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki woto HIV kuma ita ma yarinyar an auna ta an samu ta na ɗauke da wannan cuta.

Daga cikin mutane 9 da s**a yi wa yarinyar fyaɗen har da wani tsoho mai suna Musa Haru mai shekaru 60 da haihuwa wanda shima ya amsa cewa ya yi lalata da yarinyar har sau 3.

21/05/2012

hello

Address

Layin Danhassan By Hamco Hotel
Abuja

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 03:00 - 18:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 12:00 - 16:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminu Mahmoud and Brothers Nig. Ltd posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminu Mahmoud and Brothers Nig. Ltd:

Share