04/03/2026
Rundunar juyin juya halin Iran, ta bayyana cewa tana da cikakken iko da mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, inda shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya tura jiragen ruwan yaƙin Amurka domin rakiyar tankokin mai.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Fars News ya wallafa a ranar Laraba, jami’in rundunar ruwan IRGC, Mohammad Akbarzadeh, ya ce, a halin yanzu, mashigar ruwan Hormuz tana ƙarƙashin cikakken ikon rundunar ruwan Jamhuriyar Musulunci.”
Kimanin kashi ɗaya bisa biyar na danyen man fetur na Duniya ke amfani da shi, ana jigilar sa ne ta wannan muhimmiyar mashiga mai matuƙar tasiri ga tattalin arzikin Duniya.
Yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, ya na kawo tangarda ga tsarin samar da kayayyaki na Duniya, inda aka rufe zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, tare da dakatar da wasu jiragen sama masu jigilar kaya sakamakon rufe sararin samaniya a Gabas ta Tsakiya.
Rundunar ta IRGC ta bayyana cewa ba zai yiwu wani jirgi ya ratsa mashigar ba, tare da cewa an kai hari kan tankokin mai fiye da goma.