13/07/2024
Rushewar Gini da Yara Yan Makaranta A Jos🥲
YAWANCI SON BANZA KE JAWO ABIN TAKAICI, IN MUNKI JI, BAMA KI GANI BA😡
Zan fara da fassara wannan turanci da nasani tun a Jami’a wajen malamai na.
“Kuskuren Likita Mutum 1 Yake kashewa a Lokaci, Amma kuskuren Magini kan iya kashe mutum 100 a lokaci guda”
Ina cikin wannan rubutu kafin in kammala saiga wani sabon labarin rushewar wani ginin a Abuja.
Duk da ban cika son magana akan rushewar gine gine “Building Collapse” ba kasantuwar irin al’ummar da muke rayuwa a cikinta ita keson hakan kuma ba al’umma bace dake ba kwararru mahimmanci a fannin gine gine amma zan dan saka baki a wannan in kuma fadi wasu ra’ayoyi nawa a matsayina na masani kuma kwararre a fannin gine-gine.
Yanzu fisabilillahi ka dubi wannan beam dake kwance da akai circling a ginin daya rushe da yara yan Makaranta a Jos Plateau, akwai abubuwan dubawa a tattare dashi sosai na saba kaidojin gini na fitar hankali. Kai bari inma gwari gwari yanda zaka fahimta.
Abinda Yadace Abinda akai
Rodi: Y16mm. Y10mm
Links: Y10mm. Quarter rod(Y6mm). Spacing 200mm. 600mm
Yanzu fisabilillahi ta yaya wannann gini bazai rushe ba? Kar ma kaso kaga yanda akai Piloli da Slab, abin takaici.
Idan ka bincika mai ginin irin mutanen nan ne da basuson baiwa kwararrun magina da Injiniyoyi aiki, ya gwammace ya nemo birkiloli kawai aka basu aiki ayi abinda akaga dama domin kar a kashe kudi adai biya bukata kawai.
Allah shi saukaka, ya dace mutane su dawo hayyacinsu, wannan “Saving cost” din bai jawo da mai ido, idan zakai gini musamman gidan sama ka baiwa kwararru su maka ka biya su, kaima kudin aiki kai aka biya ka ka samu ko kasuwanci ba laifi bane dan kaba wani shima ya samu. Ba’a zuwa da ko kobo Qabari.
Itama gwamnati yadace ta rinka sa ido sosai, irin wannan gine gine dake dibar al’umma ba abun wasa bane, akwai abubuwa dayawa da ake dubawa kafin a yarda a yisu, ita gwamnatin tasani.
Shiyasa ni nakeda wani tsattsauran ra’ayi a sana’ata, ko waye kai kuma ko nawa gareka baka isa kabani aiki kace inyi maneji ba, saidai in bar maka aikin ka, kai nama sha barin aiki sakamakon neman tursasani domin kare sunana da tsira da mutunci na. Wallahi shekarata kusan 15 ina harkar gine gine amma ban iya maneji ba, banma san yanda ake yinshi ba in kace inyi.
Yadace a hada hannu da hannu a shawo kan wannan matsala ta rushewar gine gine domin musifa ce babba dake jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Daga karshe muna adduar Allah ya jikan wadanda s**a rasa rayuwar su, yasa a rinkayin abinda ya dace domin gujema asarar rayuka da dukiyoyi.
Anas Galadima
Jami’in Hulda da Jama’a
Makarantar Horas da Magina ta Najeriya
Reshen Jihar Kaduna.