23/12/2020
A MUTU MANA
A MUTU MURUS
Jiya Talata da rana, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi, ya rantsar da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 na jam'iyyar APC.
A wajen taron wanda ya samu halartar mabiya darikar siyasar gidan Gandujiyya,
Alhaji Abdullahi Abbas
WANDA
Tsohon kwamishina ne gwamnatin Kwankwaso
Tsohon mai bada shawara ne a harkokin siyasa a gwamnatin Ganduje
Tsohon kwamishinan muhalli ne a gwamnatin Ganduje
Daya daga cikin wanda s**a nemi sarautar Sarkin Kano ne
YA CE, su tsabar mabiya gwamna Ganduje ne, kuma idan zaben shekarar 2023 ya zo a Kano, irin abin da aka yi a shekarar 2019 shi za a maimaita, kuma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yana magana cewa a shekarar 2023 ko a mutu ko a yi, To SHI ya ce, "A mutu mana, a mutu Murus"
IRIN wannan kalamai da irin wannan siyasar, a wannan yanayin rashin tsaro da mugun talauci da ya mamaye kasa, KARYA kasa da al'umma suke yi. DOLE A GUJE SU
Miyagun kalmomi na tunzuri da isharar tarzoma da rashin daraja, babu abin da zasu haifar mana a Kano da Najeriya sai lalacewa da karin fatara da jahilci da koma wa baya.